Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya rabawa mata 2,386 tallafin awaki 7,158 a wani bangare farfado da tattalin arzikin matan karkara.
A gudanar da rabon tallafin ne karkashin shirin bunkasa noma da kiwo na KSDP, wanda bankin musulunci ke daukar nauyi.
Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an bayar da tallafin ne domin inganta sana’ar kiwo a tsakanin mata marasa karfi a fadin kananan hukumomin jihar 44.
A cewarsa, ko wacce mace za ta karbi awaki 3.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za a raba shanu 1,342 da raguna 1,822 ga mata da matasa a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na rage radadin rayuwa ga al’umma, ta hanyar fito da sabbin tsare-tsaren tallafawa al’umma.