
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya mika diyyar Naira Miliya 600 ga al’ummar unguwannin Bulbula da kuma Gayawa dake cikin Kananan Hukumomin Nassarawa da Ungogo a jihar.
Diyya kudin na gidaje da filaye ne da aka karɓa daga mazauna yankunan da zaizayar ƙasa ke addaba, domin bai wa gwamnati damar magance matsalar.
A jawabinsa a yayin bikin mika kudin, gwamna ya ce, fiye da shekaru 30 kenan yankunan ke fama da zaizayar kasa wanda hakan ke jefa su cikin mawuyacin hali musamman lokacin damuna.
“Tun da muka zo gwamnati muke duba yadda za mu kawo tallafi a gurin da matsalar take. In ji gwamnan.
“Gwamnati za ta kashe fiye da Naira biliyan 11 kan aikin, kuma za a shimfiɗa manyan bututun magudanan ruwa domin hana ambaliya musamman a lokacin damina, tare da gina sabbin hanyoyi a saman kwatocin da za a gyara. In ji gwamnan
Sannan ya kuma ce, “za a Turawa kowanne mutum kudinsa ta asusun banki”
A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar muhalli Dahir Hashim ya ce, cikin wadanda aka biya diyyar akwai wadanda gidan su ya rushe fiye da shekaru biyar.“Diyyar ta shafi fiye da gidaje 200 da filaye da masu haya da kuma masu bishiyu.” In ji shi.
Alummar yankin wadanda suka amfana da shirin sun bayyana godiyar su ga gwamnatin Kano bisa diyyar guraren su da aka basu.