
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Ya zo Kano ta’aziyyar kisan gillan da ‘yan jihar suka ya wa mafarauta ‘yan asalin jihar da kuma tabbatar da cewa za a yi adalaci a lamarin
Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya jajantawa al’ummar Kano kan abin da ya faru na kasan gilla da aka yi wa ‘yan asaalin jihar Kano a Uromi dake jihar.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya tarbe shi a gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.
“Mahaifina ya zauna a Hotoro da Gyadi Gyadi, kuma Ina yawan zuwa Kano tun Ina matashi,a dan haka ba zan bari a cutar da Kano da mutanenta ba.
“Mun zo Kano ne ni da tawagta domin mika sakon ta’aziya kan kisan gillar da aka yi wa ‘yan asalin Kano a Edo da kuma tabbatar da cewa za’ayi adalci”. In ji gwamna Okpebholo.
Gwamnan Edo ya kuma ce, a yanzu haka an kama mutane 14 da ake zargin suna da hannu wajen kashe Hausawan ‘yan asalin Kano kuma suna tsare a yanzu haka.

Sannan na ya kara da cewa, “ba dan ana hutun sallah karama ba ,da tuni an mika mutanan Abuja kamar yadda Babban Sifeton ‘Yan sandan Najeriya ya ba da umarnin hakan.”
A nasa jawabin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru a jihar ta Edo ga al’ummar hausawan na Kano, ya na mai cewa za su hada kai da gwamnan Edo domin tabbatar da adalci.
“Nagodewa gwamnan na Edo Monday Okpebholo a bisa yadda ya nuna damuwa da kuma matakan da ya dauka na tabbatar da adalci ciki har da dakatar da ayyukan ‘yan sintiri da aka samar ba bisa ka’ida ba a jihar.
“A madadin kanawan dabo muna bukatar a nunawa duniya mutanan da aka kama domin kowa ya gansu, sannan a kai su kotu, Ina kuma kira ga gwamnan Edo da ya jagoranci biyan diya ga iyalan wadanda abin ya shafa”. in ji Gwamnan Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce, zai jagoranci raka gwamnan zuwa Kananan Hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya domin jajantawa iyalan mafarautan da aka kashe a jiharsa.
Daga nan gwamna Yusuf ya sake rokon jama’ar Kano musamman matasa da su guji daukar doka a hannunsu.
Ya kuma ce a yanzu mutanan Kano sun zura ido suga irin adalcin da za’ayi kan kisan gillar da aka yi wa Hausawan na Arewa a Edo.