
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif yayi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da ya cire kwamishinan ‘yansandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda yake bijirewa umarnin gwamnan a matsayinsa na Babban mai lura da tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne wajen taron tunawa da ranar samun yancin kan kasa a filin wasa na Kofar Mata dake cikin birnin Kano a ranar Laraba
“Kwamishinan ya bamu kunya, saboda halayyar da ya nuna wadda ta sabawa yakamata, kuma wadda ke cike da son rai da rashin kwarewa, a irin wannan rana mai matukar tarihi ga al’ummar Kano da ma na Najeriya baki daya…” in ji gwamnan.
Abba Kabir Yusif ya bayyana damuwa kan yadda ‘yansandan Kano karkashin kwamishina Ibrahim Bakori suka janye tsaro a wajen taron duk kuwa da umarnin hakan da gwamnan ya bayar ga Kwamishinan.
An gudanar faretin ban girma a filin wasan na Sani Abacha kamar yadda aka saba a bisa al’ada duk shekara.
A wannan bikin taron faretin ya samu halarta manyan jami’an gwamnati da sauran jami’an tsaro da ‘yan makaranta da kuma kungiyoyin sa kai.