Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar kaduwa da alhini bisa rasuwar ‘yan Majalisar dokokin jihar guda biyu, Sarki Aliyu Daneji da Aminu Sa’ad Ungogo, wadanda da suka rasu a rana guda.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu.
Gwamna Yusuf ya bayyana rasuwar a matsayin wani babban rashi mai tada hankali a tarihin Kano, yana mai cewa mutuwar ‘yan Majalisar biyu cikin lokaci kaɗan ta jefa gwamnati da al’ummar Kano cikin jimamin da ba za a iya misalta shi da kalmomi ba.
A cewar gwamna Abba , marigayan biyu sun kasance jajirtattun masu hidima ga jama’a kuma wakilai ne masu amana, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen wakiltar al’ummomin su da hidimar jihar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa, mutuwar ta su ta bar gibi mai wahalar cikewa a Majalisar dokokin ta Kano da yankunan su.
