
Wata gobara da tashi a safiyar Larabar ta kone kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.
Kasuwar wadda ake kira da Kwalema na kan titin zuwa Zango daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC.
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri.
Aminiya ta rawaito cewa, kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.