
Gobarar ta tashi ne a ginin Gidan Ado Bayero dake matsugunin Jami’ar Northwest a kofar Nassarawa a Kano
Bayanai sun nuna gobarar ta tashi da misalin karfe 12 na ranar Alhamis.
Wakilinmu da ya je jami’ar domin ganewa idonsa ya taras da wani jami’in tsaron jami’ar da ya samu rauni yayin taimakawa jami’an kashe gobarar ta hanyar da za su shiga ciki, ya yi masa karin bayani kan yadda wutar ta tashi.
“Wuta ce ta tashi a hawa na tara, a lokacin da ta fara mun dauka a hawa na goma ne. Da muka hau wurin sai muka taras ashe ba a wannan hawan bane.
“Sai muka dawo hawa na tara duk mun dauko abin ‘kashe wuta ‘fire extinguisher’ mun yi yunkurin mu kasheta, ashe ta fi karfin a kashewa da wannan abin, kafin jami’an hukumar kashe gobara su zo, wutar ta yi karfi.” In ji Jami’in tsaron da bai bayyana sunansa ba.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da tashin gobar ya kuma ce, tuni Jami’an suka isa wajen domin shawo kan ta, kuma zai yi karin bayani bayan sun kammala bincikensu.