
Gobarar dajin mafi muni a tarihin Isra’ila na cigaba da ruruwa duk da daukin gaggawa na kashe gobarar daga kasashe 5.
Fiye da tawagogi 150 na jiragen saman kashe gobara na ci gaba da kokarin kashe wutar amma abin ya gagara.
Rahotanni na cewa wutar na ƙara ruruwa sakamakon kaɗawar iska mai ƙarfi da kuma ƙaruwar yanayin zafi.
Hukumar kashe gobara ta ƙasar ta ce ta samu nasarar kashe ɗaya daga cikin gobarar dajin da ta tashi a yankin Birnin Ƙudus.
Firmayimnistantan ƙasar Benjamin Netanyahu tuni ya ayyana gobarar a annoba dake bugatar agajin gaggawa.
Ana ta kokarin kwashe mutanen daga babban birnin. Hukumomi sun ce an kama mutum takwas bisa zargin hannu a tashin gobarar.
To sai dai ƴansanda sun mutum uku kawai aka tsare, kuma dalilin tsare su ba shi da alaƙa da tashin gobarar.