Hagu, Kabiru Maikaba sakatare da tsakiya Khalid Musa da dama, Auwalu Mashal Mataimakin shugaba.
Gidauniyar Kannywood ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci harkokin kungiyar.
An gudanar da zaben ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, a ofishin gidauniyar da ke Kano, bayan karewar wa’adin tsofaffin shugabannin kungiyar karkashinin jagorancin Shu’aibu Yawale.
Malam Khalid Musa tsohon marubuci a masana’antar kuma tsohon mataimaki na musamman kan masana’antar Kannywood ga gwamna Ganduje, shi aka zaba a matsayin sabon shugaban gidauniyar.
Yayin da tsohon jarumi kuma Auwalu Isma’il Marshall ya zama Mataimakin Shugaba da Kabiru Maikaba a matsayin Sakatare.
Tsohon marubuci kuma mai bada umarni a finafinai Bala Anas Babinlata shi aka zaba a matsayin Daraktan Ayyuka, sai tsohon dan jarida kuma marubuci Yakubu Liman a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a.
Kwararren mai horas da ‘yan wasa kuma mai kwalliya Shehu S. Bello ne ya koma matsayinsa na Mai Binciken Kudi na gidauniyar da sai Adamu Mohammed da aka zaba a matsayin Ma’aji, da Ahmed Alkanawi a matsayin Daraktan Sayayya.
Gidauniyar Kannywood kungiya ce mai zaman Kanta mai gabatar da ayyukan jin kai da ke da rajista a Hukumar CAC.
Sabbin shugabanni su na da wa’adin shekaru uku na gudanar da ayyukansu cikin manufofin kungiyar.
