Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce shawarar da ɗansa, Abba Abubakar, ya yanke na shiga jam’iyyar APC ra’ayin kansa ne.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce a tsarin dimokuraɗiyya, irin wannan zaɓi ba sabon abu ba ne kuma ba abin daga hankali ba ne, ko da koda an samu banbancin ra’ayi irin wannan.
Ya ce a matsayin sa na ɗan dimokuraɗiyya, ba ya tilasta wa ’ya’yansa kan ra’ayinsu, haka nan kuma ba zai tilasta wa al’ummar Nijeriya ba.
Sai dai Atiku Abubakar ya ce Abin da ya fi damunsa shi ne rashin kyakkyawan shugabanci karkashin APC da kuma tsananin matsin tattalin arziƙi da na zamantakewa da ta dora wa al’umma.
Ya kuma ce yana nan daram wajen aiki tare da ’yan ƙasa masu kishin ƙasa irinsa domin dawo da nagartaccen shugabanci da kuma gabatar wa ’yan Nijeriya ingantacciyar makoma da za ta kawo sauƙi, da ci gaba
