
Kasar Burtaniya ta yi fatali da ikirarin kafa sabuwar gwamnatin soja a Sudan da shugaban dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya yi.
Gwamnatin Ingila na mai cewa wannan ba zai kawo karshen yakin basasar kasar ba, wanda ya yi sanadiyyar mummunan rikici na tsawon shekaru biyu.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Burtaniya ta fitar a yau Laraba, ta bayyana cewa hadin kan kasar na da muhimmanci, wanda ya kamata a martaba ‘yancin gashin kanta. Burtaniyan ta ƙara da cewa raba Sudan gida biyu ba zai kasance alheri ba ga ci gaban kasar.
Mohamed Hamdan Dagalo, jagoran dakarun RSF, ya ayyana kafa sabon gwamnatin sa, yana mai cewa wannan mataki na ballewa daga gwamnatin Janar Abdel Fattah al-Burhan ne, wanda ke fafatawa da shi a neman shugabancin kasar.
Yakin na sudan ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula, yayin da miliyoyin mutane suka rasa muhallansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yanayin a Sudan a matsayin mafi muni a duniya, tare da mika kira ga duniya domin taimakawa.