Rundunar yan sandan jihar Bauchi tace tana gudunar da bincike kan wani jami’in ta mai suna Yusuf Ibrahim wanda ake zarginsa da hallaka wani jami’in soja da bingida.
Kakakin rundunar yan sandan jihar CSP Ahmad Muhammad wakil ya ce alamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Augusta a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Ya kara da cewa, wata tawagar kwararro da suka hada da yan sanda da soja suna ci gaba da gudunar da bincike domin gano dalilin da ya sanya jami’in dan sandan yayi harbi.
Rundunar yan sandan tayi alkawarin gurfanar da duk wanda aka samu da hannu kan wannan zargin a gaban kotu domin fuskatar shari’a.
