
created by photogrid
An bayyana gayyatar sarkin Kano da Babban Sifeton ‘yan sanda ya yi zuwa Abuja don amsa tambayoyi kan kisan da aka yi a bikin salla da cewa cin mutuncin Kano.
Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa (Northern Youth Assembly) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar wacce kakakinta na kasa Kwamared Mohammed Hussaini ya sa hannu ta ce, aika takardar gayyatar amsa tambayoyi ga sarkin ba karamin cin mutunci bane ga masarautar da daukacin sarkunan arewa.
“Muna masu da amfani da wannan dama mu tunatar da rundunar ‘yansadan ta kasa da cewa, Mai martana sarkin Kano Muhammadu Sunusi na ba II na da daya daga cikin ma su kima da dararja da kuma mutunci a jerin sarakunan kasar nan.
“Duk wani yunkuri na tozarta masarautar Kano ta hanyar wannan gayyata don kawai farantawa wasu makiya jihar ba zamu lamunta ba”. In ji sanarwa.
Kungiyar ta alakanta gayyatar sarkin zuwa hedikwatar ‘yansanda ta kasa da rikicin danbarwar masarautar ta Kano, ta kuma ce hakan shiri ne na wasu a gwamnatin tarayya na haddasa fitina a jihar wanda ba za ta lamunta ba.
Sanarwar ta yi kira ga jama’ar Jihar da su kwantar da hankalinsu kar su bari irin wannan mataki na tsokana ya sa su yi abin da bai dace ba.
A ranar Juma’a ne Babban Sifeton ‘Yansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya aika da takaradar gayyata ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusiu na II zuwa Hedikwatar ‘Yansandan don amsa tambayoyi kan kisan dan bijilante da aka aka yi yayin rakiyar sarki bayan sallar Idi.
Babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun ya bada umarnin gayyatar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II zuwa Abuja don gudanar da bincike kan rikicin da aka samu a ranar Sallah, lamarin da ya janyo rasuwar wani matashi.
An aika da wasikar gayyatar ta hannun Kwamishinan ‘yan sanda mai lura da ayyuka na musamman Olajide Rufus Ibitoye, ya kuma bukaci Sarkin ya bayyana a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025, da karfe 10:00 na safe.
.