
Shugaban jam’iyyar APC Dakta Abdullahi Umar Ganduje CON ya karbi jiga-jigan jam’iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Cikin wadanda shugaban APC ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta. Baffa Bichi da kuma tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Danbatta da Makoda Honorabul Badamasi Ayuba.

Sauran sun hada da Honorabul Abdullahi Sani Rogo da Zubairu Hamza Masu da Muhammad Diggol da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da kuma Abbas Sani Abbas.
