Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara ta Kano, Injiniya Sani Bala Danbatta ne ya Tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.
Ya ce an karɓi sunayen wuraren da za a kai taransifomomin daga kananan hukumomi sama da 30, kuma ma’aikata na ci gaba da aikin tantance wuraren kafin a fara girkawa.
Ya ƙara da cewa an riga an fara aikin girka wasu a Kura, Gwale da Dala, inda aka kammala a wasu unguwanni tun makonnin da suka gabata, yayin da ake tattaunawa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) domin haɗa kai wajen kammala aikin.
