
Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi II ya nada Alhaji Munir Sunusi Bayero a matsayin Galadiman Kano, Yayin da shi ma Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Sunusi Ado Bayero a matsayin Galadima.
An yi nadin sarauntar Alhaji Mannir a gidan Rumfa, fadar sarkin Kano Muhammadu Sunusi, yayin da shima Sarki Aminu Ado Bayero yayi nasa nadin a gidan sarki na Nassarawa duk a safiyar yau juma’a.

Wakilinmu na masarautar Kano Ammar Wakili Shanono, ya ruwaito mana manyan baki a yayin bikin nadin sarautar sun hada da gwamnnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo da wasu daga cikin Kwamishioni da shugabannin kanannan hukumomin Kano.
Yayin da Sarki Sanusi ke nada sabon Galadiman Kano, ita ma fadar Nasarawa ta Sarkin Kano na 15, tana nada Alhaji Sanusi Bayero a matsayin Galadima.

Wannan na nufin yayin da ake takaddama a kan Sarkin Kano, sabuwar takaddama za ta kunno kai a kan sarautar Galadima.
Sakataren yada labaran fadar Sarki Aminu Ado, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya tabbatar wa da Premier radio cewa an nada sarautar cikin kwanciyar hankali.