
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce, cire tallafin man fetur ya sa gwamnatinsa ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi daga asusun tarayya sau uku.
Shugaban na magana ne a yayin taron shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a Abuja ranar Talata da dare, Tinubu ya lissafa abubuwan da ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnatinsa damar yi.
“Jihohi suna samu ninkin kason kasafin da suke samu daga gwamnatin tarayya har sau hudu”. In ji shi.
Shugaba Tinubu ya nanata cewa, sauyin da gwamnatinsa ke yi ya zama dole, idan ana son kasar nan ta dore a cikin wadata.
Sai dai cire tallafin da shugaban yayi a ranar da aka rantsar da shi a 2022 ya haifar da hauhawan farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.