Rasha ta ce tana sa ido sosai dangane da barazanar Amurka na daukar matakin soja kan Najeriya
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova ce ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Moscow a ranar Juma’a.

Babbar Jami’ar ta bukaci Washington da dukkan bangarorin da abin ya shafa su mutunta dokokin kasa da kasa da kuma ikon cin gashin kai na kasashe.
A ranar 1 ga Nuwamba, Trump ya yi ikirarin umurnin hedkwatar tsaro na Pentagon da ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai harin soja a Najeriya.
Labarai masu alaka
Kalamansa sun haifar da damuwa a kasashen duniya, ciki har da Rasha, wacce ta jaddada cewa dole ne a kiyaye ikon kowace kasa da cin gashin kanta.
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani tun daga lokacin.
Ministan Harkokin Wajen Najeria Yusuf Tuggar, ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai da kuma barazar Amurka na iya haifar da tashin hankali.
Ya kuma bukaci kasashen duniya da kada su maimaita kura-kuran da suka haifar da rikici a Sudan.
