
Dakataccen Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya bukaci al’ummar jihar akan su kwantar da hankalinsu tare da bin doka don zama lafiya, yayin ya ke kokarin bin matakan da doka ta tanada don tabbatar da dimokuradiyya ta ci gaba da wanzuwa a jihar.
Fubara ya fadai hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema Labarai a ranar Talata da dare.
Gwamnan da shugaba Tinunbu ya dakatar da dokar ta baci ya ce, dama alummar jihar Rivers sun yi fice wajen zaman lafiya don haka su yi amfani da wannan damar da karfin dimokuradiyya wajen ganin komai ya warware cikin sauki ba tare da an tayar da jijiyar wuya ba.
“Duk da irin rashin jituwar siyasar dake tsakaninna da wasu zababbu, hakan bai saka an kasa samun shugabanci nagari a jihar ba.
“Hakan kuma bai dakatar da albashin ma’aikata ba, domin duk wata ina kokarin kowa ya samu nasa, abin dake kara nuna cewa ni mai son zaman lafiya da tabbatar da adalci ne.” In ji shi.

Dakataccen gwamnan ya bayyana takaicinsa kan yadda tarihin jihar ya sauya ta hanyar daukar wasu matakai da shugaban kasa ya ke yi na ganin su ne daidai, kuma mafita ga halin da jihar ke ciki.