Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, don halartar taron samar da tsarin ci gaba mai dorewa.
A yayin taron, shugaba Tinubu zai tattauna da shugabannin Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da mai da hankali kan karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ana sa ran a ranar Alhamis 16 ga watan Janairu zai dawo Najeriya.