Ɗaruruwan Falasɗinawa ne suka bazu a kan tituna a Gaza domin nuna rashin amincewa da ƙungiyar Hamas, inda suke neman ta sauka daga mulki.
Sai dai wasu mayaƙan ƙungiyar ɗauke da bindigogi da sanduna, fuskokinsu a rufe sun tarwatsa masu zanga-zangar.
Masu goyon bayan ƙungiyar sun kare ta, sun kuma nuna rashin tasirin zanga-zangar tare da kiran masu boren da cewa maciya amana ne.
ƙungiyar ta Hamas ba ta ce komai a kan lamarin ba.
