
Al’ummar falasdinawan da ke Gaza sun nuna jin dadi da farin ciki sanarwar yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin Isra’ila da Hamas a Gaza.
Labarin cimma yarjejeniyar ya yadu a yankin da Isra’ila ta yiwa kawanya, musamman a yankin Khan Younis a kudancin Gaza a inda mutane suka fito tituna suna murna da fatan wannan zai zama silar samun sauki daga hare-haren Isra’ila.
Yarjejeniyar tsagaita wutar da Shugaban Trump ya sanar a daren Laraba, na zama mataki na farko na shirin kawo karshen yakin da ya dauki shekaru biyu ana gwabzawa.
Yarjejeniyar ta bukatar sakin fursunonin Isra’ila da ke hannun Falasdinawa a Gaza a madadin sakin Falasdinawa da ke hannun Isra’ila, yayin da dakarun Isra’ila za su janye zuwa wani layin da aka amince da shi, a cewar Trump.
Gidan talabijin na Al Jazeera ya ce, akwai alamun samun sauki ga jama’ar Gaza gaba daya inda ya bayyana lokacin a matsayi wani abu muhimmi na tarihi.