
Jakadan Algeria a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Amar Bendjama ya nemi afuwar Falasɗinawa bayan da ya ce an kange duk wani yunƙurinsu na kai ɗauki ga halin da suke ciki.
Jakadan ya fadi hakan ne a ranar Alhanis a birnin New York, bayan tashi daga zaman kwamitin sulhu na Majalisar Majalisar Dinkin Duniya.
Aljazeera ta ruwaito Benjamin na cewa Falasɗinawa Maza da Mata su yafe musu sakamakon yaƙin kusan shekaru 2 da Isra’ila ke ci gaba da ƙaddamarwa a kansu da zuwa yanzu ya kashe mutanen da yawansu ya tasamma dubu 66 sun kuma kasa tabuka komai.
“Ku yafe mana saboda mun gaza, mun gaza isar da ƙoƙarinmu gareku, ku yafe mana saboda yunƙurinmu da kuma kyawawan aniyarmu ta gaza isa gareku saboda shingayen da ke tsakaninmu’’. In ji shi
Tun farko wasu ƙasashe 10 ne suka miƙa ƙudirin da ke buƙatar sake zama don tafka muhawara game da shirin tsagaita wutar a Gaza lura da halin da ake ciki, ƙudirin da ya samu amincewa 14 cikin mambobin kwamitin na dindidin 15 amma Amurka ta hau kujerar naƙi.
Ƙarƙashin daftarin da aka tafka muhawara akansa, an buƙaci dakatar da yaƙin nan bisa sharaɗin tsagaita wuta na dindindin wanda dole dukkanin ɓangarorin na Isra’ila Hamas su aminta da shi da kuma sakin ilahirin fursunonin da ƙungiyar ke tsare su.
Zaman tafka muhawarar na jiya shi ne irinsa na farko da aka ga kwamitin ya yi tun faro kisan ƙare dangin na Isra’ila a Gaza a wani yanayi da masana a ɓangaren jinƙai ke cewa halin da Isra’ilar ta jefa Falasɗinawan yankin Gaza shi ne mafi munin azabtarwa da wata al’umma ta taɓa fuskanta akan idon duniya.
Sai dai Amurka, kamar yadda aka yi tsammani ta sake hawa kujerar naƙi, inda jakadiyar ƙasar a gabas ta tsakiya Morgan Ortagus ke cewa wasu daga cikin bayanan da ake fitarwa ga duniya game da halin da Falasɗinawa ke ciki babu gaskiya a ciki.
Ortagus ta ce wajibi ne Hamas ta saki ilahirin mutanen da ta kama yayin harin ranar 7 ga watan Oktoba gabanin fara batun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta, sai dai jim kaɗan bayan wannan zama, Hamas ta fitar da sanarwar da ke cewa matakan da Isra’ila ke ɗauka na sake jefa rayukan fursunoninta a haɗari wanda ke nuna matuƙar wahala su iya komawa ga iyalansu.