
Fadar shugaban ƙasa ta karyata jita-jitar cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na fama da rashin lafiya.
Wani rahoton cibiyar binciken rahotonni ta ƙasa da ƙasa (ICIR) ya ruwaito cewa wasu majiyoyi sun bayyana cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na shirin fitar da shi ƙasashen waje domin kulawar gaggawa saboda rashin lafiya.
Rahoton ya ce “Tinubu ya kwanta rashin lafiya na kwanaki, abin da ya sa bai halarci wasu muhimman ayyukan gwamnati ba, inda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a wasu taruka”.
Wata majiya ta kuma shaida cewa an soke wasu daga cikin shirye-shiryen shugaban ƙasa tun farkon mako, tare da share wasu sauran jadawali domin likitoci su bibiyi lafiyarsa sosai.
Sai dai mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce labarin ba shi da tushe, yana mai cewa Tinubu na nan yana aiki yadda ya kamata. A ranar 5 ga Agusta na ziyarce shi a ofishinsa, yana aiki,” in ji shi.
Da jaridar Daily Trust ta tuntube shi a daren jiya, Onanuga ya sake musanta jita-jitar, yana cewa babu wata matsala da lafiyar shugaban ƙasa, kuma yana iya zaɓar yin aiki daga gida ko daga duk inda ya ga dama.
ICIR ta bayyana cewa lokacin ƙarshe da aka ga Tinubu a bainar jama’a shi ne ranar Juma’a, 1 ga Agusta