
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwararewa ta kasa ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwana biyar daga yau, bisa ga matsayar da aka cimma a majalisar zartarwar ƙungiyar.
Ƙungiyar ta bukaci dukkan mambobinta a cibiyoyi daban-daban su bi wannan umarni ba tare da kaucewa ba.
A cewar kungiyar, matakin yajin aikin ya zama dole ne domin matsa lamba ga gwamnati kan buƙatunsu na inganta walwala da kyautata yanayin aiki, tare da tabbatar da ingantacciyar tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.
Ta ce makasudin yajin ba wai cutar da al’umma ba ne, sai dai domin tabbatar da nagartar harkar lafiya a kasa
Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin mambobinta a wannan lokaci, inda ta ce nasarar wannan mataki zai dogara ne akan yadda kowa zai tsaya tsayin daka wajen aiwatar da yajin aikin.
Sai dai Kungiyar ta ce za ta ci gaba da lura da yadda lamarin zai kaya a wannan mako, sannan a ƙarshe za ta tantance matakan gaba dangane da yadda gwamnati za ta amsa buƙatunsu.