
Babban attajirin na duniya wanda kuma a baya-bayan ta babe tsakaninshi da Shugaba Trump, bayan ya kasance babban kusa a gwamnatin – Elon Musk, ya tsaya kan matsayinsa na neman a tsige shugaban daga mulki.
Sai dai ya janye barazanar da ya yi ta ficewa daga wani muhimmin shirin Amurka na sararin samaniya.
Hamshakin attajirin ya sauya shawara ne ‘yan sa’o’i bayan ya ce zai soke aikin kumbon zuwa sararin samaniya da ya yi wa lakabi da SpaceX Dragon.
Wannan rigima ta barke ne har ta kai aka ga tsofaffin shakikan biyu a rana – bayan hamshakin attajirin wanda mako daya baya yake zaman lamba daya da kusan ba kamarshi a gwamnatin ta Trump, bayan ya soki shugaban kasar kan sababbin dokokinsa kan haraji, da kuma kudurin dokar gwamnatin na kashe kudade.
Cikin wani saƙo da hamshaƙin attajirin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi wa Trump gori da cewa ba don taimakonsa ba da Trump din ya fadi zaɓen shugaban ƙasar.
Bugu da kari ya goranta wa Shugaba Trump da cewa in ba don taimakon da ya bayar ba da tuni Trump din bai ci zabe ba, kuma jam’iyyar hamayya ta demokrats ce ke da rinjaye a majalisar dattawan ƙasar.
Mista Musk – wanda ajiye aikinsa a gwamnatin Trump a makon da ya gabata – ya zargi Shugaba Trump da rashin godiyar Allah.
To sai dai a martanin da shugaba Trump ya mayar ya ce Elon Musk ya ba shi kunya, yana mai cewa attajirin ya fara sukarsa ne bayan da ya yanke tallafin da ake bai wa ababen hawa masu amfani da lantarki.
