Ya kuma ce, kotun tarayya a hukunci na farko ta wuce huruminta, yi kuma yikira da hukunta alkalin da yanke shari’ar
Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya mika sakon taya murnar ga sarki Kano Muhammadu Sunusi a bisa samun nasarar hukuncin da yayi a Kotun Daukaka Kara a Abuja
El Rufa’i ya mika sakon ne ta shafisa na dandalin sada zuminta na X a ranar Juma’a.
Nasir El Rufa’I ya kuma ce Kotun Tarayya ta kauce huruminta a inda ta sa baki a shari’a da ya shafi masarautun da ba a baban birnin tarayya ba ne.
“Babu ruwan Babban Kotun Tarayya da batun da ya shafia masarautu in ba a babban birnin tarayyya bane.” Inji shi
Sannan ya soki alkalin da kakkausar harshe da sauraron shari’ar da kuma yanke hukunci da ya kira “na son zuciya da kuma abin kunya”.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Kula da Alkalai ta Kasa da hukunta alkalin.
A cikin hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta yi, ta ce a dawo da shari’ar Kano, kuma Alkalin Alkalai na jihar ya nada wani alkalin ya sake sauraron shari’a tun daga farko, ya kuma yanke hukunci cikin gaggawa