
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaryata zargin cewa yana ƙarƙashin jagorancin siyasar tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai, inda ya ce shugabannin da suka yi masa jagoranci tun farko sun haɗa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma marigayin lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Cif Gani Fawehinmi.
Gwamnan ya bayyana hakana ne a hirarsa da gidan talabijin na TVC a farkon makon nan.
“Ba na ganin dacewar na tsaya ina musayar kalamai kan batun jagoranci, ina mai jaddada cewa burina shi ne samar da ingantaccen mulki ga al’ummar Kaduna”. In ji gwamnan Uba Sani.
Gwamnan ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa gwamnatinsa tana biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙarya da wasu ’yan siyasa ke yaɗa wa don samun abin faɗa.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa tana amfani da dabarun tsaro ta fuskar Soji da kuma ta hanyar tattaunawa tare da shugabannin al’umma domin shawo kan matsalolin tsaro, musamman a Birnin Gwari, inda ya ce tsarin haɗin kai na al’umma ya fara haifar da sakamako mai kyau.