
Hukumar yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagonsa EFCC ta tsare ɗan’uwan shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, Sirajo Salisu Usman, bisa zarginsa da hannu cikin badakalar Naira biliyan 50 a kudaden aikin Hajji.
Sirajo, wanda ke matsayin Mataimakin Darakta a ofishin shugaban hukumar, ya sha amsa tambayoyi tun farkon wannan watan tare da wasu manyan jami’an NAHCON.
Binciken EFCC ya danganta shi da asarar Naira biliyan 25 wajen biyan kudin tantunan Masha’ir, Naira biliyan 8 wajen gidajen ajiyar mahajjata a Makka, da kuma Naira biliyan 1 da miliyan dari shida 6 da aka kashe wajen daukar matan jami’an NAHCON a shekarar 2025 kadai.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa hukumar ta kama masaukin gaggawa 6,500 a Makka da ba a yi amfani da su ba, abin da ya janyo asarar kusan Naira biliyan 8.
Tun daga 7 ga watan Agusta, EFCC ta sha tambayar wasu manyan jami’an hukumar, ciki har da lauyin NAHCON, Barrister Nura Danladi, da kuma wasu daraktoci. A ranar 19 ga watan nan, hukumar ta kuma tsare wasu kwamishinoni biyu, ciki har da na kudi da tsare-tsare.
Wani jami’in hukumar ya shaida wa Daily trust cewa, duk wata takardar hukuma Sirajo ne ke yi wa shugaban bayaninta kuma shi ke sanya hannu.