
Kotun Majistiri mai lamba 15 da ke Nomansland a Kano ta ba da umarni ga Mataimakin Babban Sufeton Yan sanda mai lura da shiyya ta ɗaya da ke Kano da yayi bincike kan fitaccen ɗan jaridar nan kuma babban Editan jaridar Daily Nigerian Jaʼafar Jaʼafar da wakilin jaridar Umar Audu bisa zargin ɓata suna.
Umarnin kotun ya biyo bayan ƙorafin da Abdullahi Ibrahim Rogo, Babban Jamiʼin Tsare-tsaren Gwamnan Kano ya shigar ta hannun lauyoyinsa.
Lauyoyin Rogon sun gabatar wa kotu ƙorafi, inda suka zargi Jaʼafar da Umar da wallafa rahotanni a shafin Daily Nigerian a ranar 22 da 25 ga Agusta, 2025, da suka danganta Rogo da almundahanar kuɗi har naira biliyan 6.5.
Lauyoyin sun ce waɗannan rahotanni ƙage ne da aka shirya domin bata suna da zubar da ƙimar Rogon.
A takardar umarnin da mai shari’a Abdulaziz Habib Mahmud ya bayar mai dauke da kwanan watan 28 ga Agusta, kotu ta umurci ofishin mataimakin Babban Sufeton ƴan sandan shiyya ta ɗaya da ke Kano da ya binciki waɗanda ake zargin.
Idan za ku tuna dai Daily Nigerian ta wallafa rahoton zargin Rogon da karkatar da kuɗaɗen Gwamnati zuwa asusunsa wanda ta bayyana daga hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC, kuma bayan rahoton nasa ICPCn ta yi ƙarin bayani kan lamarin.