Gwamnan jihar Borno Babagana Ummara Zulum ya bada umarnin hana sayara da Man fetur a Karamar Hukumar Bama Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara Kan Yada Labarai, Dauda Iliya ya fitar wanda ya bayyana cewa wannan mataki yana cikin dabarun da gwamnatin jihar ta dauka domin yaki da ayyukan ta’addanci.
Sanarwa ta ce, an dauki wannan mataki ne bayan shawarwari da hadin gwiwa da hukumomin tsaro don shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
Umarnin dakatar da sayar da fetur din zai hada da cikin garin Bama da Banki da kuma sauran yankunan dake karamar hukumar nan take.
Gwamnan ya yi gargaɗi cewa duk wanda aka kama yana karya wannan doka zai fuskanci cikakken hukuncin doka.
Gwamna Zulum ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar, tare da kiran jama’a da su ba da goyon baya da haɗin kai a ci gaba da yaki da ta’addanci.
