A Jamhuriyar Nijar, ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan da suka yi ritaya ta bayyana damuwarta kan matsalolin da ƴan fansho ke fuskanta wajen karɓan hakkokinsu.
Ƙungiyar ta ce tun bayan ƙaddamar da bincike kan ma’aikatan da suka yi ritaya, da dama daga cikinsu sun daina samun fansho.
Sakataren ƙungiyar ƴan fansho na ƙasar, Mahamadou Moussa, ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka yi ritaya sun shafe sama da wata 10 ba tare da sun karɓi kuɗin fansho ba.
