Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wasu manyan kwamandojin kungiyar Ansaru biyu, wata kungiyar ta’addanci da ake zargin tana da alaƙa da Al-Qaeda, bisa zarginsu da hannu wajen kai munanan hare-hare akasarnan.
Wadanda ake zargin sune Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas/Mukhtar, wanda aka bayyana a matsayin Sarkin Ansaru, da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda dukkan su an kama sune a kwanan nan a yayin gudanar da ayyukan tsaro.
A cewar hukumar laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.
Ana zargin mutanen biyu da hannu a harin da aka kai gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, inda fursunoni fiye da 600 da suka hada da wadanda ake zargi da Boko Haram suka tsere.
Ana sa ran gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja nan ba da jimawa ba a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar.
Gurfanar da su gaban kotun na zuwa ne makonni uku bayan Mai Baiwa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya sanar da kama su.
Ribadu ya ce mutanen biyu sun kasance cikin jerin sunayen ‘yan Nijeriya da aka fi nema ruwa a jallo tsawon shekaru, inda suka jagoranci kai hare-hare da dama kan fararen hula, jami’an tsaro, da muhimman ababen more rayuwa.
