U.S. President Donald Trump looks on as he meets with the White House Task Force on the FIFA World Cup 2026 in the Oval Office at the White House in Washington, D.C., U.S., November 17, 2025. REUTERS/Evelyn Hockstein
Amurka ta ɗage takunkumin da ta sanya wa man Iran – wanda tuni yake cikin jiragen ruwa a teku – na wucin-gadi.
Ta yi hakan ne domin rage illar da yaƙin ke haifar wa a kasuwar makamashi.
Matakin na tsawon kwana 30 ya shafi man da aka riga aka loda ne a jiragen ruwa, kafin, ranar Juma’a 20 ga watan Maris din nan.
Sakataren Baitul- Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce hakan zai sa a samu gangar mai miliyan 140 a kasuwar duniya.
A ba ya ma Amurkar, ta dage takunkumin da ta sanya a kan man Rasha wanda tuni yake teku.
