Matashin ɗan kasuwa a Najeriya, Alhaji Ibrahim Abubakar da ke neman karrama shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, bisa gudummawar da yake bayarwa ga harshen Hausa, ya ce dole ne a jinjinawa Tchiani saboda aiwatar da muhimman ayyuka na ci gaba da tausayi ga al’ummar ƙasarsa da kuma jagoranci abin koyi.
Alhaji Ibrahim, ya ce ya ji daɗin yadda Janar Tchiani ya rage farashin shinkafa, man fetur, siminti da sauran kayan masarufi domin sauƙaƙa wa al’ummar Nijar.
Cikin jerin matakan sauƙin rayuwa a Nijar, akwai rage kuɗin asibiti, tabbatar da bayar da magani kyauta ga yara yan ƙasar masu ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu haihuwa, tare da rage kuɗin makarantu masu zaman kansu, tun da na gwamnati kyauta ne.
Alhaji Ibrahim Abubakar ya kara da cewa irin wannan sauƙaƙe farashin kayayyakin yau da kullum ya nuna cewa shugabancin Janar Tchiani na cike da tausayi da kishin jama’a.
Saboda haka, ya jaddada aniyarsa ta kai ziyara ƙasar Nijar domin karrama Shugaban bisa irin waɗannan nagartattun halaye da muhimman ayyuka, da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa harshen Hausa.
Haka kuma, Alhaji Ibrahim Abubakar ya yi kakkausar suka ga mutanen da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yi wa Shugaban Ƙasar Nijar kalaman batanci, musamman bayan ya tallafa wa jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Malam Nata’ala.
Ya bayyana cewa shugaba mai tausayin jama’a irin Janar Tchiani ba ya nuna bambanci wajen taimakawa al’umma, ko dan Nijar ne ko ba dan Nijar ba.
Don haka, ya shawarci masu irin waɗannan kalamai da su yi hattara wajen tozarci akan Mutum mai mutunci da karamci Janar Abdourahmane Tchiani.
Dole ne a Jinjinawa Tchiani saboda aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba da tausayi ga al’ummar kasarsa da kuma jagoranci abin koyi – Alhaji Ibrahim Abubakar
