
A ranar ta biyu ta dokar kulle da Gwamna Umaru Muhammad Bago ya sanya a jihar Neja, al’umma na nuna damuwa kan yadda matakin ya dakile harkokin kasuwanci da sufuri a jihar.
Dokar ta takaita zirga-zirgar babura da adaidaita sahu daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, a matsayin mataki na dakile fadan daba da kwacen waya da kuma fashi da makami da jihar suka addabi jihar musamman Minna babban birnin jihar.
Sai dai, mafi yawan jama’a na ganin wannan mataki a matsayin kuntatawa ga wadanda ba su da hannu a matsalar tsaro, maimakon magance batagarin da ke haddasa rikicin.
Mazauna yankunan da wannan dokar ta shafa sun bayyana cewa batagarin sanannu ne ga jami’an tsaro, suna ganin ya fi kyau a kama su maimakon sanya dokar kulle ga kowa.
Dokar ta janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin cewa ba za a iya magance matsalar tsaro ba ta hanyar sanya dokar kulle da ba ta ware tsakanin masu laifi da wadanda ba su da hannu.