
Yusuf Galambi tare da Shugaban APC Ganduje a ofishinsa
Shine dan jam’iyyar a Majalisar Tarayya na farko da ya yi hakan a bisa zargin baraka tsakanin Agbo da kuma Kwankwaso
Yusuf Shitu Galambi, Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa,. ya sauya sheƙa zuwa APC.
Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar.
“Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu sakamakon rigimar mulki tsakanin iyayen jam’iyyar da suka kafa Moses Agbo da kuma Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso jagora Kwankwasiyya.
A inda bangaren Agbo dake ikirarin halarcia ya sanar da korar Kwankwaso da Buba Galadima da kuma sauran mukarrabansa daga jamiyyar.
Guguwar sauya jam’iyya a ‘yan kwanakin nan ta sa ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a cewar masu sharhi kan al’amuran kasar nan
Idan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Aminiya