Dan majalisar tarayya mai walkiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin kudi da tsare-tsare na majalisar wakilai, Engr. Abubakar Kabir Bichi FOE, ya kara biyawa daliban karamar hukumar masu karatun digiri na biyu da digiri na uku a jami’ar Northwest da ke Kano kudin makaranta.
Kudin da ya biyawa daliban su 11 na zangon karatu na 2024 zuwa 2025 ya kai Naira miliyan daya da dubu dari da tamanin da hudu da goma sha shida.
Kwana biyu kafin wannan, dan majalisar ya biyawa daliban karamar hukumar ta Bichi da ke karatu a jami’ar Ahmadu Bello Zaria kudin makaranta.
Wata sanarwa da mashawarci ga dan majalisar a fannin yada labarai da hulda da yan jarida, Jamilu Halliru Master, ya fitar, ta ce shekaru sama da biyar kenan Eng. Abubakar Bichi ya na biyawa dukkan daliban dake karatu a makarantun gaba da sakandare kudin makaranta ba tare da nuna banbancin yare, addini ko siyasa ba.
Shugaban kwamitin Ilimi na Engr. Abubakar Kabir Bichi wato Dr. Habibu Usman Abdu Bichi, ya yiwa dukkan daliban fatan samun nasara a karatun da su kasa gaba.