
Daya daga cikin wadanda Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke nema ruwa a jallo dangane da badakalar kasuwancin Crypton na CBEX, ya mika kansa ga hukumar domin fuskantar bincike.
Jami’in mai suna Adefowora Abiodun ya isa ofishin EFCC a Abuja a yammacin ranar Litinin tare da lauyansa, domin ba da hadin kai kan binciken da ake gudanarwa.
Wannan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin kamo Adefowora tare da wasu abokan huldarsa na CBEX Seyi Oloyede, Emmanuel Uko, da Abiodun Olaonipekun.
Ana zargin su da gudanar da harkar kasuwancin Crypto ta hanyar da ba ta dace ba, tare da damfarar daruruwan mutane na miliyoyin naira.
EFCC ta hannun lauyarta Fadila Yusuf, ta shigar da karar mutanen gaban kotu, tana zargin cewa sun kirkiri kasuwancin CBEX da nufin yaudarar masu zuba jari, lamarin da ya haifar da asarar da ta kai fiye da naira tiriliyan daya (₦1tn).
CBEX na daya daga cikin kasuwancin da suka ja hankalin masu zuba jari da alkawurran riba mai tsoka, sai dai hukuma ta ce tsarin ya zama wata kafar damfara da ya ci gaba da cutar da ’yan kasa da dama.
EFCC ta ce za ta ci gaba da bin diddigin duk wadanda ke da hannu a cikin badakalar har sai an gurfanar da su gaba da shari’a.