Kungiyar ECOWAS ta sanar da ficewar tawagarta daga Guinea-Bissau bayan da Shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi barazanar korarsu.
Dambarwar siyasa ta ɓarke ne kan wa’adin mulkin Embalo, inda ‘yan adawa ke cewa ya kamata ya ƙare makon da ya gabata.
Sai dai Kotun Koli ta ƙasar ta ce wa’adinsa zai ƙare ne a ranar 4 ga Satumba.
A ranar 23 ga watan jiya, Embalo ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa zai gudana ne a 30 ga Nuwamba.
ECOWAS ta ce tun ranar 21 ga watan jiya ta aike da tawagarta tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, don shiga tsakani kan shirin zaɓe.
Amma da safiyar Asabar, tawagar ta fice daga ƙasar bayan barazanar Embalo.
A halin yanzu, an ga Shugaba Embalo yana ganawa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a birnin Moscow a wata ziyara da ya kai a makon da ya gabata.
