
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya bayyana dalilinsa na soke shirinsa na gudanar da bikin hawan sallah
Sarkin bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta hanyar bidiyo da ya fitar a ranar Laraba da dare a fadarsa ta gidan Nassarawa.
Sarkin ya ce, ya ɗauki dakatar da hawan ne sakamakon shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi da kuma gudun kar a zubar da jini.
“Malamai da dattawa sun shawarce mu, kuma muna mutunta su. Don haka, bayan nazari tare da majalisar masarauta, mun yanke shawarar cewa mun janye domin zaman lafiya,” in ji shi.
“Idan akwai fargabar cewa hawan salla zai haddasa tashin hankali da asarar rayuka ko dukiyoyi, toh, yana da kyau a daina,” in ji shi.
Sarkin ya jaddada cewa bikin hawan salla ba abu ne da ya zama wajibi ba idan zai iya haddasa rikici da asarar rayuka. Ya kuma bai wa magoya baya da sauran masoya hakurin wannan mataki da ya dauka wanda ya ce don a zauna lafiya ne.
Tun farko, sarakunan biyu dake taqaddama kan sarautar, Muhammadu Sanusi na II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba da tashin hankali a jihar Kano.
A makon da ya gabata ne Aminu Ado ya aike wa ’yan sanda takardar sanarwar gudanar da hawan salla bayan da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya umarci Muhammadu Sanusi II da ya shirya yin hawan salla a karshen watan Ramadana a bisa al’ada.
Ana sa ran wannan matakin zai rage fargabar da ake ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano