
Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin litar man fetur da take sayar wa ƴan kasuwa daga Naira 890 zuwa Naira 825.
Matatar ta ce, ta ɗauki mataki ne domin sauƙaƙa wa al’umma gudanar da rayuwa a dai-dai lokacin da suke shirye-shiryen fara azumin Ramadan.
Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar Alhamis
A bisa wannan tsarin mazauna Lagos za su rika sayen litar man a kan Naira 860 a gidajen Mai MRS, yayin da za a rika sayar da shi kan Naira 870 a sauran jihohin kudu maso yamma.
A arewa za a rika sayar da litar a kan Naira 880, sai yankin kudu maso kudanci da kudu maso gabas da za su rika sayen litar a kan Naira 890.
Ba wannan ne karon farko da matatar mai ta Ɗangote ke rage farashin litar man fetur ba, inda a farko-farkon wannan wata na Fabairu, ta rage Naira 60.
Haka zazalika, a watan Disambar bara, Ɗangote ya rage farashin litar da Naira 70.50, inda mutane suka rika sayen man a kan Naira 899 daga Naira 970.