Shugaban kasuwar canjin kudi ta Wapa a Kano ya tabbatar da cewa, farashin Dalar Amuka ya tashi a kasuwar bayan dawowa daga bukuwan Sallah karama.
Jami’in hulda da jama’a na biyu na kungiyar Hussaini Sani Musa ne ya bayyan haka a tattaunawarsa da manema labarai.
Ya ce a halin yanzu kasuwa na ci gaba da bukatar Dalar wanda ya yi sanadiyar karuwarta daga Naira 1400 gabanin sallah wanda yanzu haka ake canzar da ita akan Naira 1,410.
Masu sana’ar canjin a kasuwar na bayan fage na hasashen cewa duk da bukatar da yan kasuwa ke yiwa Dalar , baza a samu karuwar ta ba sosai la’akari da wadatarta.
