
iHukumomin lafiya a Bauchi sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 58, sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Sun kuma ce an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar.Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki da cutar a jihar ta Bauchi.
Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda barkewar cutar ke ci gaba da kashe mutane, lalata rayuwar jama’a, da kuma jefa tsarin kiwon lafiya na jihar cikin matsala.
“Ana iya kaucewa wannan barkewar cutar idan aka ɗauki matakan gaggawa, aka haɗa kai wajen tunkarar cutar, tare da ci gaba da inganta ruwa, tsafta da kula da muhalli yadda ya kamata.” In ji shi.