Ana sa ran nan ba da jimawa ba, magaji ga zuriyar Zia masu tasiri a siyasar Bangladesh, Tarique Rahman, zai dawo gida bayan shafe shekara 17 yana gudun hijira.
Rahman, wanda shi ne shugaban jam’iyyar siyasa mafi girma a kasar, Bangladesh Nationalist Party (BNP), kuma ɗan tsohuwar Firaminista Khaleda Zia, zai dawo ne gabanin babban zaben da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairu.
Jam’iyyar BNP ta bayyana cewa ta kammala shirin tarbar jagoranta, inda ta ce tana sa ran mutane miliyan biyar za su hallara a babban birnin Dhaka domin taron maraba da shi.
A cewar jam’iyyar, Rahman zai yi jawabi ga magoya bayansa a wurin taron.
