Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya gargadi cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, yara 420,000 na iya mutuwa daga cikin yara miliyan 3.5 da ke fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki a Nijeriya.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatef ce ta yi wannan gargadin a lokacin ziyararta ofishin UNICEF na Maiduguri a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Abdelatef ta ce sai an hanzarta samar da kuɗi da kayan abinci na cikin gida da kuma faɗaɗa cibiyoyin jinya, idan ba haka ba Nijeriya na iya rasa dubban ɗaruruwan yara ta hanyar yunwa, cututtukan da za a iya kauce musu, da kuma rashin kulawa.
Ta ƙara da cewa yankin Arewa maso Gabas na ci gaba da fama da rikicin jinƙai inda mutane fiye da miliyan 4.5 ke cikin matsananciyar buƙatar tallafi.
A game da ilimi kuma, Abdelatef ta jaddada cewa Nijeriya na da matsaloli ta wannan ɓangaren sosai, inda yara miliyan 18.3 ba sa zuwa makaranta—miliyan 10.2 daga cikinsu yara ne masu shekarun firamare, yayin da miliyan 8.1 ke da shekarun ƙaramar sakandare.
A ɓangaren rigakafi da kuma tsirar yara, Abdelatef ta bayyana cewa Nijeriya na da yara fiye da miliyan 2.1 da ba a taɓa yi wa rigakafi ko ɗaya ba, adadin da ya fi kowace ƙasa a duniya.
