
A kalla mutane 24 yan ta’adda suka kashe tare da sace wasu mutum 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara.
Kungiyar al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa yan ta’addan sun kai hare-haren ne kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban.
Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura.
A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo da Katangar Gabas Bilbils.
A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a Tabkin Rama, Matsafa, da Ruwan Gizo, yayin da Rafin Jema a Gummi da ƙauyukan Adabka da Masu a Bukkuyum suma suka fuskanci hari.
Kungiyar ta jaddada cewa ci gaba da kai hare-hare yana nuna bukatar gaggawa ta ƙarfafa matakan tsaro domin kare al’ummomin karkara daga hannun ‘yan bindiga da ke addabar jihar.