
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi sanar da kama wani matashi dan shekara 30, bisa zargin kashe wani ɗan Achaɓa tare da sace mashin dinsa,
A wata sanarwa da kakakin rundunar CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar tare da rabawa manema labarai, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Oktoba, a unguwar Dakta Sulaiman Adamu da ke bayan tsohon filin jirgin sama na Bauchi.
Matashin mai suna Basiru Mohammed, ya halaka dan acaba mai suna Mamuda Zakari Yau, domin samun kuɗin da zai yi auri mace ta uku, in ji sanarwar
“ ‘Yan sandan sun garzaya da Mamuda Zakari zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tabawa Balewa dake cikin garin Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
“An kuma ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawa na asibitin domin gudunar ci gaba da gudunar da bincike kan lamarin.” In ji Kakakin a cikin sanarwar.
Kwamishinan ‘yan sanda jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin dawo da batun babban sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike tare da aika wanda ake zargi a gaban kotu da zaran an gama.