
A yau Juma’a ne Shugaban ƙasa Bola Ahmad zai zo jihar Kano domin ta’aziyyar rasuwar Aminu Alhasan Dantata.
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fita ya ce, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan ziyara a matsayin alamar haɗin kan ƙasa da girmamawa ga al’ummar Kano da tarihin marigayi Alhaji Aminu Alasan Dantata.
Ya kuma yi kira ga jama’ar Kano da su tarbi shugaban ƙasa Tinubu cikin mutunci da al’adun girmama baki da jihar ke da su.