Dokokin za su taimakawa gwamnatotin jihohi azamar farfado da tattalin arzkinsu ne, in ji shi
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kudirorin gyaran haraji da ta bijiro da su, za su taimaka wajen ingiza gwamnoni su farfado da tattalin arzikinsu.
Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da jaridar The Nation.
Ya kuma jaddada cewa kudirin zai zaburar da gwamnoni su dauki matakan da su ka dace domin kara samar wa jihohinsu kudin shiga.
Haka kuma Ministan ya musanta zargin da wasu ke yi na cewa, an bijiro da kudirin ne domin muzgunawa wani sashe na Najeriya.
Idan za a iya tunawa dai, batun kudirin haraji ya na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a Arewacin Najeriya, inda gwamnoni irinsu gwamnan Bauchi, Bala Mohammed kudirin zai lalata tattalin arzikin Arewa.
